How the Air Car Works


 


At first glance, the idea of running a car on air seems almost too good to be true. If we can use air as fuel, why think about using anything else? Air is all around us. Air never runs out. Air is nonpolluting. Best of all, air is free.


Unfortunately, air alone can't be used as a fuel. First, energy has to be stored in it by squeezing the air tightly using a mechanical air compressor. Once the compressed air is released, it expands. This expanding air can be used, for example, to drive the pistons that power an engine. The idea of using compressed air to power a vehicle isn't new: Early prototypes of an air-powered vehicle go back to the middle of the 19th century, even before the invention of the internal combustion engine.

Hausa language:

KARATUN MU A YAU.


Kimiyya da fasaha dai ta zame wa dan adam abin dogaro don ci gaban rayuwansa da kuma kawo maslaha a da yawa daga cikin matsalolinsa. 


To a wannan karatun mu na yau zamu yi dubi ne ga wani ci gaban da aka samu a wannan fanni na ilimi. Wannan ci gaba kuwa shi ne na kirkiran mota mai amfani da iska maimakon man fetir. 


Ita wannan mota mai amfani da iska mai makon fetir kamfanin volkswagen dake kasar jamus shi ya kirkiro ta.


 Ita wannan mota tana amfani ne da iska wanda aka tara shi a cikin wani tanki, shi wannan iska wani na'ura ne wanda ake kiransa da suna air inflator shi yake cika iskan wanda ya kai sama da 30kg.


A lokacin da wannan motan fetir ya kare mata sai shi wannan iska dake cikin tankin zai fita da karfin gaske, wanda a cikin injin a kwai wani farfela wanda iskan yake bugansa sai ya fara juya piston na motar ta yadda sashin injin zai fara juya driving shaft na motar, wanda daga nan kuma motar zata iya yin tafiya.


Irin wannan motar ana kiransu da suna compressed air vehicle Wato mota mai amfani da iska wanda aka tarashi makir a tanki.


 Kamfanin Volkswagen sunce ita wannan motar asali tana amfani ne da fetir . A lokacin da injin yake aiki yana tara iskan ne a wani tukunyar ma'ajiyar iska (air tank). Idan fetir din ya kare sai injin motar ya koma amfani da wannan iskar dake cikin tankin a maimakon fetir.


Kamfanin sunce tana iya tafiyar kilometer 30 kafin iskan ya kare. Wanda hakan ya nuna cewa zaka iya isa wajen da zaka samu gidan man fetir wanda zaka sha.


 Sunce shi wannan kimiyar suna so su inganta shi ta yadda za su duba yiwuwar amfani da fiber wajen sanyashi a matsayin tankin dake tara iskan domin hakan zai ragewa motar nauyin tankin . Domin sunyi amfani ne da tanki na karfe wanda suna da fahimtar ya karawa motar nauyi.


Kamfanin volkswajen suna ganin wannan kimiyar zaitaimaka sosai wajen samun saukin makamashin mayi domin akwai wani ma'aji wanda yana jiran kota kwana. 


ALLAH shine mafi sani.

Post a Comment

Previous Post Next Post